MUhimman dalilai 10 da zai sa ka yi amfani da Ayoba

AMFANI KYAUTA

Amfani da Ayoba kyauta ne. Kana bukatar data domin tura sakonni da files zuwa kontak din ka, amma wasu network din (kamar MTN) za su iya bada data kyauta su ma.

RABAWA NUNA KULAWA CE

Raba faifan bidiyo, audio, da dai sauran su tare da kontak din ka.

SADARWA CIKIN SAURI

Yi amfani da littafin tara adireshin ka don sadar da kai da wadanda ke cikin kontak din ka cikin sauri da sauki.

KIRA

Kira ta amfani da manhajar ta hanyar yin Magana.

YI CHAT YANZU

A take aika ko kuma karbi sakon text da sakonnin murya daga duk wanda ke kontak din ka.

AMINTACCE

Kudundine sako daga farko har karshe na nufin wani daban ba zai iya karanta sakonnin da ke cikin hirar ba.

CHATIN DA KOWA

Tura sakon text ga duk wanda ke cikin kontak din ka, ko da yana da, ko bai da Ayoba.

MU HADU

Nuna inda ka ke a kowane lokaci wa mutanen da ke kontak din ka.

CHAT DIN KUNGIYA

Iya yawan ku, iya jin dadin ku! Shirya chat na kungiya don ku yi magana da yan uwa da abokanai cikin sauki a chat guda.

TRANSFER DIN KUDI

Aika ko karbar biyan kudi ta hanyar Mobile Money (Ya na nan tafe).

Game da mu

Ayoba manhajar aikewa da sako ce a take,

mutanen Afrika suka kirkira ta domin yan Afrika.

Duk da kasancewar Afrika nahiya guda, ta zamo gida ga daruruwan al’adu. Muna alfahari da wadannan banbance-banbacen da ke Afrika, ta hanyar samar da ingantacciyar manhajar aikewa da sako da ta dace da bukatun mutanen ta da kuma fatan su.

Tun da farko, Ayoba ta samar da sahihiyar hanyar kudundine bayanai domin tabbatar da adana bayanan masu amfani da manhajar cikin sirri. Wannan na nufin cewa dukkanin sakonni da ke cikin hirar, wani daban ba za a iya karanta su ba, ko da ma’aikacin Ayoba ne. 

Yadda mu ke gudanar da aikin fasaha na nufin mutanen da ke amfani da Ayoba, za su samu damar yin magana da kowa ta hanyar amfani da wayar hannu, ko da kuwa basu kai ga samun manhajar Ayoba ba.

A yanzu, kowa zai iya sauke Ayoba a wayar hannu da ke dauke da manhajar Android (amfani da sauran manhajoji da kuma wasu na’urori na zuwa nan gaba ba da dadewa ba!). Bugu da kari, muna da hadin gwuiwa da MTN, wannan na nufin za mu iya samar da datar Ayoba kyauta* ga dukkan masu amfani da MTN a lokacin da suka tura sakonni, hotuna, fai-fan bidiyo da dai sauransu, zuwa ga mutanen su. Kuma, dukkan amsoshi daga sakonnin Ayoba za su kasance kyauta* ga masu amfani da MTN, ko da ba su amfani da manhajar.

Me Ayoba ta sa gaba

Muna da kirkire-kirkire masu ban sha’awa da muka tsara nan da yan watanni domin bunkasa ayyukan mu a fadin Afrika. Wannan ya hada da samar da hanyoyin aikewa ko karbar kudi cikin Ayoba, zuwa ga mutanen da ke kundin adana lambobi da ke Afrika ta hanyar Mobile Money.