Frequently Asked Questions (FAQ)

FARAWA / SHIRIN FARAWA

Goyon Baya

Idan kana/kina bukatar taimako ko kana/kina son tuntubar Tawagar Ayoba din, taimaka kaje/kije Ayoba.me/contact

Saukewa da Shigarwa

Ta yaya zan sauke manhajar Ayoba?

 •  Ayoba.me/download- (data kyauta); ko

Zaka/zaki iya zuwa adireshin yanar gizo na Ayoba domin sauke manhajar a kowanne lokaci, Indan mai amfani da MTN ne kai/ke, zaka/zaki iya sauke manhajar Ayoba a kyauta, ba tare da amfani da kudin datar ka/ki ba.

 • Google Play store

Za kuma ka/ki iya sauke Ayoba daga Google Play Store. Kawai bude Play Store, binchika Ayoba, sai ka sauke shi domin fara amfani da Ayoba.

Yaya zan sabunta Ayoba?

Za’a iya sabunta Ayoba akan Google Play Store

Manhajar ta Ayoba ana iya samun tane kawai a kan wayoyin android a halin yanzu. Domin sabuntawa, jeka/jeki Google Play Store, sannan sai ka/ki dannan Jeri > Manhajojina da wasanni. Dannan SABUNTAWA dake kusa da Ayoba! Tura sako nan take a kyauta.

Ta wata hanyar kuma, jeka/jeki Play Store sannan ka/ki binchika Ayoba. Danna SABUNTAWA a karkashi Ayoba! Tura sako nan take a kyauta.

Akan adireshin yanar gizo na Ayoba

Za kuma ka/ki iya sabunta manhajar Ayoba din ka/ki akan adireshin mu na yanar gizo, kawai jeka/jeki Ayoba.me/download.

Ta yaya zan iya kara shigar da manhajar Ayoba?

Domin kara saka manhajar Ayoba, da farko akwai bukatar ka/ki goge shi daga wakayar ka/ki. Kafin ka/ki yi hakan, muna baka/baki shawarar ka/ki ajiye hirarrakin ka/ki. Kawai danna madannin Jeri, sannan sai ka/ki danna Saiti, sannan sai ka/ki danna gyare-gyare sai ka/ki zabi Ajiyar Hirarraki.

Tabbas wannan zai ajiye maka/miki hirarrakin ka/ki a ma’ajiyar yanar gizo, ya kuma baka/baki damar dawo da duk hirarrakin ka/ki idan da bukatar hakan. Ka/ki kula da cewar, ajiyar ka/ki ba a cikin na’urar ka/ki suke ba, saboda haka zaka/zaki bukaci damar shiga yanar gizo domin yin ajiya.

Taimaka kabi/kibi wadannan matakan don gogewa da kuma kara saka manhajar Ayoba:

Zabi na daya 1:

 • Danna ka/ki rike dan hoton manhajar Ayoba a fuskar wayar ka/ki har sai dan hoton ya fara girgiza
 • Taba wannan X din dake sakon dan hoton manhajar Ayoba din.
 • Danna ‘Goge’ domin cire manhajar da duk wasu kayan ta
 • Danna madanni na bangon waya 
 • kara sauke Ayoba daga Google Play Store.
 • Dawo da ajiyar hirarrakin ka/ki ta hanyar danna madannin Jeri, sannan sai ka/ki zabi saiti, sannan ka/ki danna gyare-gyare sai ka/ki zabi Ajiyar Hirarraki, da dawo dasu.
 • Zaka kuma ka/ki iya zuwa adireshin yanar gizo na Ayoba domin saukewa da kuma kara shigar da manhajar a kowane lokaci. Indan mai amfani da MTN ne kai/ke, zaka/zaki iya sauke Ayoba a kyauta*, ba sai kayi/kinyi amfani da datar ka/ki ba.

*A lokacin garabasa

Zabi na biyu 2:

 • Taba ka/ki rike dan hoton manhajar Ayoba din dake kan fuskar wayar, sannan ka/ki ja shi ka/ki ajiye shi a cikin kwandon shara/kwandon cire manhaja.
  • Zabi cirewa domin tabbatar da gogewar, don cire manhajar da duk wasu kayan ta.
  • Danna madanni na bangon waya
  • kara sauke Ayoba daga Google Play Store.
 • Dawo da ajiyar hirarrakin ka/ki ta hanyar danna madannin Jeri, sannan sai ka/ki zabi saiti, sannan ka/ki danna gyare-gyare sai ka/ki zabi Ajiyar Hirarraki, da dawo dasu.
 • Zaka kuma ka/ki iya zuwa adireshin yanar gizo na Ayoba domin saukewa da kuma kara shigar da manhajar a kowane lokaci. Indan mai amfani da MTN ne kai/ke, zaka/zaki iya sauke Ayoba a kyauta*, ba sai kayi/kinyi amfani da datar ka/ki ba.

*A lokacin garabasa

Tabbatarwa

Ta yaya zan iya tabbatar da lamba ta?

Da ka/kin gama sauke manhajar, sai ka/ki bude ta ka/ki bi wannan matakan:

 1. Shigar da cikakken sunan ka/ki
 2. Zabi kasar ka/ki daga lis din da ya sauko. Wannan zai kuma cike maka/miki tsarin lambar kasar ka/ki a lambar wayar ka/ki da kan sa.
 3. Shigar da lambar wayar ka/ki a akwatin dake kasa.
 4. Danna ‘Tabbatar’ don neman tsarin lambobi.
 5. Shigar da tsarin lambobi shidan 6 da ka/ki samu ta hanyar sako.

Ban samu tsarin lambobi shidan 6 ba ta hanyar sako.

 • Jira ma’aunin lokacin ya kare sannan ka zabi ‘Sake Tura Sako’.
 • Kar ka/ki chanki tsarin lambobin, idan ba haka ba za’a rufe maka/miki sashen ka/ki na tsawon wani lokaci. Wannan wani salon tsaro ne don kare sashen ka/ki ta yadda wani bazai iya shiga ba.

Idan matsalar ta cigaba, yi kokari ka jarraba wadannan:

 • Sake tashin wayar (Domin sake tashin wayar, kashe ta, jira sakan talatin, sannan sai ka/ki kara kunna ta).
 • Goge ka/ki sake saka sabon samfurin manhajar ta Ayoba.

Zan iya amfani da Ayoba akan na’urori biyu?

Sashen ka/ki na Ayoba, zaka/zaki iya tabbatar da shi ne da lamba daya bisa waya daya kadai. Idan kana/kina da waya mai LAYI biyu, ka/ki sani cewa duk da haka dole lamba daya zaka/zaki zaba don tabbatarwa a Ayoba. Babu wani zabi na mallakar sashen Ayoba da lambobi biyu.

Akwai bukatar sai na kara yin rijista idan na cire sannan kuma na mayar da manhajar?

A’a baka/bakya bukata. Abinda kawai kake/kike bukata shine ka/ki kara sauke Ayoba daga Google Play Store ko kuma daga Ayoba.me/download. Shigar da sunan ka/ki, zabi kasar ka/ki daga jerin lis din da ya sauko, shigar da lambar wayar ka/ki sannan ka/ki zabi ‘Tabbatar’.

Ka/Ki kula: Idan ka/kin ajiye hirarrakin ka/ki na baya kafin ka/ki goge manhajar ka/ki kuma sakawa, hirarrakin ka/ki na baya zasu dawo da kansu.

AMFANI DA AYOBA

Sarrafa Sashe da Bayanan Mutum

Ta yaya zan iya saka ko sabunta hoton sashe na?

Idan baka/baki riga ka/kin zabi hoton sashen ba:

1. Bude jeri a bangaren hagu daga sama a manhajar.

2. Danna alamar gyara

3. Danna hoton sashen > Alamar kyamara.

4. Zabi hoto daga ma’ajiyar hotunan ka/ki don amfani dashi a matsayin hoton sashen ka/ki.

Idan dama kana/kina da hoton sashe a halin yanzu:

 1. Bude jeri a bangaren hagu daga sama a manhajar.
 2. Danna hoton sahen ka/ki ko kuma alamar gyara.
 3. Idan ka/kin zabi alamar gyara, to danna hoton sashen ka/ki > alamar kyamara
 4. Zabi hoto daga ma’ajiyar hotunan ka/ki don chanja hoton sashenka na yanzu.

Zan iya sabunta Sunana da ake Gani?

 1. Bude jeri a bangaren hagu daga sama a manhajar.
 2. Danna sunan ka/ki da ake gani ko kuma alamar gyara sannan sai ka/ki gyara ko ka/ki saka sabon sunan ka/ki da ake gani.

Ta yaya zan iya saka ko sabunta matsayin da nake ciki?

 1. Bude jeri a bangaren hagu daga sama a manhajar.
 2. Danna bangaren matsayin ka/ki ko kuma alamar gyara.
 3. Sanya sabon matsayi (status) sannan ka/ki zabi alamar yarda don ka/ki tabbatar, ko kuma ka/ki zabi matsayin ka/ki daga lis din matsayoyin da ka saka a baya.

A kula: Idan ka/kika toshe lamba, wannan mutumin bazai iya ganin hoton sashen ka/ki ba ko kuma sabuntawar matsayin ka/ki.

Ta yaya zan iya goge sashe na?

Akwai wasu matakai kaɗan masu sauki da zaka/zaki bi idan ka/kika yanke shawarar goge sashen ka/ki. Ka/ki kula cewa wannan tsarin ba za’a iya chanja shiba bisa kowanne irin hali, ko da su kansu ƙungiyar Ayoba dinne, saboda haka ya kamata ka/ki tabbatar cewa wannan shine abinda kake/kike son kayi/kiyi.

Bi wadannan matakai guda hudu:

 1. Bude manhajar Ayoba din
 2. Bude jeri a bangaren hagu daga sama a manhajar.
 3. Saitin Sama > Gyare-gyare > Goge sashen ka/ki
 4. Tabbatar ta hanyar danna EH.

Goge sashen ka/ki zai:

 • Goge sashen ka/ki an Ayoba har abada
 • Goge tarihin hirarrakin ka/ki.
 • Cire ka/ki daga dukkanin kungiyoyin ka/ki na Ayoba, nan take.

Wasu muhimman abubuwa da za’a kula da su:

 • Baza ka/ki samu damar shiga sashen ka/ki ba
 • Goge sashen ka/ki bazai shafi bayanan da sauran masu amfani da manhajar ke da ba.
 • Kofi na wasu kayayakkin (misali; tarihin al’amura) na iya zama a ma’ajiyar mu amma an kaba su da abubuwan da zasu saka a gane mutum.

 

 

 

 

Zan iya amfani da Ayoba akan sabuwar waya ta?

Idan zaka/zaki koma daga waya daya zuwa wata wayar, kuma tare da cigaba da amfani da lambar ka/ki, zaka/zaki ajiye bayanan sashen ka/ki. Sashen ka/ki yana hade ne da lambar wayar. Kawai sauke manhajar Ayoba akan sabuwar wayar sannan sai ka/ki tabbatar da lambar wayar ka/ki.

Idan zaka/zaki koma daga waya daya zuwa wata wayar, kuma ba tare da ajiye lambar ka/ki ba, sauke manhajar Ayoba akan sabuwar wayar sannan sai ka/ki tabbatar da sabuwar lambar wayar.

Ta yaya zan iya chaja yare akan manhajar Ayoba?

Don chanja yaren wayar ka/ki:

Android: Jeka/Jeki saitin wayar ka/ki > Tsari > Yaruka & Kayan Aiki > Yaruka. Danna ka/ki zabi yare.

Idan kana/kina amfani ne da wayar Android, za ma ka/ki iya chanja yaren Ayoba daga cikin manhajar. Don yin hakan, kawai danna jeri sannan sai ka/ki zabi saiti sai kuma ka/ki danna gyare-gyare.

FARASHI/KUDIN BIYA

Kudin da Masu amfani da Ayoba za su biya

Nawa ne farashin aika sako ko kuma sakon fayal dake kunshe da murya ko hoto ko hoto mai mutsi a Ayoba?

 Ayoba na amfani da yanar gizon wayar ka/ki (4G / 3G / 2G / EDGE ko Wi-Fi) wajen turawa da kuma karbar sakonni daga abokai da yan uwa. Yanayin datar da ake ja wajen turawa da karbar sakonni ya danganta ne da irin tsarin da kake/kike yi da kamfanin sadarwar ka/ki. Sannan ka/ki tabbatar da cewa baka/baki karar da iyakar datar ka/ki ba. Ta wani bangaren kuma, zaka/zaki iya amfani da Ayoba yayin da ka/kika jona zuwa cibiyar sadarwar Wi-Fi, wadda zata iya zama ta kyauta.

 Ayoba sun hada gwiwa tare da MTN, kamfanin sadarwa mafi girma a Afirka, don samar da datar Ayoba a kyauta* ga abokan ciniki MTN (bisa la’akari da manufofin saukakawa na amfani da suka dace). Wannan na nufin cewa abokan ciniki na MTN zasu iya aikawa da kuma karɓar saƙonni a rubuce, sauti, bidiyo, hotuna da fayal-fayal a akan manhajar Ayoba ba tare da samun ƙarin farashin data ba.

*A lokacin gabatar da garabasa

Nawa ne farashin kiran waya ta hanyar amfani da Ayoba?

Za ka/ki iya yin kiran waya daga manhajar Ayoba zuwa ga wani a cikin lambobin ka/ki na Ayoba. Za’ai cajin kiran kamar yadda ake cajin ainahin kiran waya kuma zaiyi amfani da katin wayar ka/ki ko kuma mintunan da kake/kike dashi. Abu mafi muhimmanci, yin kira a cikin manhajar ba ya amfani da data kuma ba kyauta bane.

Farashin wandanda basa kan Ayoba.

Akwai bukatar sai na kasance inada manhajar Ayoba sannan zan iya aika ko kuma karɓar saƙonnin daga abokai da yan uwa wadanda suke amfani da Ayoba?

 Ayoba yafi aiki da kyau idan kana/kina magana da wani daban wanda ke da Ayoba a wayar su. Dalilin haka, mun yi ƙoƙari na musamman wajen ganin an tafi da kowa da kowa, kuma ba kamar sauran manhajojin sakonni ba, za ka iya yin magana da kowa ba tare da la’akari da cewa sunada manhajar Ayoba ko basu da ita ba.

Saƙonni da aka aika ta hanyar Ayoba zuwa lambobin sadarwar ka/ki waɗanda ba su da manhajar Ayoba, za’a aika su zuwa garesu a matsayin rubutattun sakonni na SMS, kuma zasu kunshi hanyar da zasu bi wajen zuwa yanar gizo don ganin hoto ko fayal-fayal a shafinsu na yanar gizo.

A yawancin ƙasashe, haɗin gwiwarmu tare da MTN yana nufin cewa idan abokinka/kawarki abokin dan tsarin MTN ne, za su iya amsa maka/miki sakon ka/ki ta yin amfani da rubutaccen sako na SMS, kuma zaka/zaki karbi wannan sakon amsar lafiya lau cikin manhajar Ayoba naka. Abotarmu da MTN na nufin cewa dukan waɗannan rubutattun sakonnin martanin na SMS za su zama kyautane idan ka/kike aika.

Amma duk da haka, idan abokin/abokiyar harkar ka/ki ba dan/’yar tsarin MTN bane/bace, za su iya karɓar saƙonnin ka/ki daga Ayoba ta hanyar rubutaccen sakon na SMS, amma ba za su iya mai da martanin amsa ga saƙon da suka karba ba. Za a sanar da su game da wannan iyakancewar. Abu mafi kyau shine abokan harkar ka/ki su sauke manhajar Ayoba.

Menene farashin idan bani da manhajar Ayoba akan na’ura ta?

Idan ka/kin kasance mai amfani da MTN ne kai/ke, kuma baka/baki da manhajar Ayoba a kan wayar ka/ki zaka/zaki iya yin martanin amsa ga rubutaccen saƙon da aka karɓa daga masu amfani da Ayoba, kuma rubutaccen sakonku na SMS zai zama kyauta.

Idan kai/ke ba mai amfani da MTN bane/bace, zaka/zaki karbi saƙonnin Ayoba ta hanyar rubutaccen sako na SMS amma ba zaka/zaki iya maida martanin amsa ba. Kasance cikin cikakken jin dadin Ayoba ta hanyar sauke manhajar daga sashen manhajoji na Google (Play Store) ko kuma a Ayoba.me/download.

Amfani-ba-tare-da-data ba, za’a yi shine na iya lokacin da aka tanada na garabasa, sannan manufofin saukakawa na amfani ka iya shigowa.

Idan kai/ke mai amfani ne na MTN zaka/zaki iya sauke manhajar Ayoba a kyauta, a yanzun nan a sashen Ayoba.me/download. Ko kuma za ku iya ziyartar Google Play Store.

TSARO

Shin babu wata matsala a amfani da Ayoba?

Don ajiye bayanan ka/ki cikin tsari da kuma tabbatar da sirrin ka/ki Ayoba sunyi amfani da ingantacciyar hanyar kare zantuttukan ka/ki daga bango-zuwa-bango. Wannan ya tabbatar da cewa daga kai/ke sai wanda (ko wadanda) kuke zantuka da su ne kawai zaku iya karanta abinda aka tura. Babu wani wanda zai iya karanta zantukan ku, har su kansu ‘yan kungiyar Ayoba din.

Kwarai ya tabbata cewa baza mu taba bada bayanin ka/ki ga wani ba tare da umarnin ka/ki ba. Zaka/zaki iya canza saitin sirrin ka/ki ta cikin manhajar ta hanyar zaben sakwanni daga cikin jerin saitin, sannan sai a danna Sirri. Sannan kuma muna shawartar ka/ki da ka/ki duba sharrudan mu na sirri a Ayoba.me/termsandconditions.

Wayyoyi da suka bata ko aka sace

Wayata ta bata ko an sace, me ya kamata nayi?

 • Idan wayan ka/ki ta bata ko an sace, zamu iya taimaka maka/miki wajen kulle sashen ka/ki daga amfanin da ba izini. Taimaka ka bi matakan dake kasa
 • Muna kuma kara tunatarda kai/ke cewar ka/ki sanar da kamfanin sadarwar ka/ki da gaggawa don su rufe layin ka/ki saboda ya hana wani amfani da wayar. Yayin da aka kulle layin ka/ki, ba zaka/zaki samu damar tantance sashen ka/ki na Ayoba da wannan lambar ba, tunda kana/kina bukatar samun rubutaccen sako na SMS don kammala tantancewar.

Hanyoyi biyu da zaka/zaki iya bi:

 • Yi amfani da sabon Layi dake da lamba iri daya (watau suwafin) don ka/ki tayar da sashen ka/ki na Ayoba a sabuwar wayar ka/ki. Wannan ce hanya mafi sauri wajen dakatar da sashen ka/ki dake kan wayar da aka sace. Shi Ayoba za’a iya tabbatar dashi ne da lambar waya guda daya akan na’ura daya a lokaci guda.
 • Tuntube mu akan Ayoba.me/help sannan kuma a cike takardar bada bayanai tare da rubuta “Bata/Satar Waya a sama. A taimaka a rufe sashena” sannan kuma ka hada da lambar wayar ka a cikakken tsari na kasa-kasa kamar yadda akai bayani a nan.

A kula: 

Yana da muhimmanci ka/ki tuna cewa ko da layin ka/ki a kulle yake, idan wani zai iya samun damar amfani da wayar ka/ki da kuma manhajar Ayoba din, za’a iya amfani dashi ta hanyar jona wayar da yanar gizo ta iska. Kungiyar Ayoba din basu da damar kashe Ayoba daga gurinsu. Saboda haka muna shawartar ka/ki da ka/ki tuntube mu da bukatar kashe shashen Ayoba da wuri-wuri.

Ka/ki sani cewa kungiyar Ayoba basu da damar nemo inda wayar ka/ki take, don haka baza mu iya taimaka maka/miki ka/ki nemo wayar ka/ki. Wayar ka/ki na iya kasancewa tana da wata manhajar da zata iya taimaka maka/miki wajen nemota ta daga wata wayar…

Idan ka/kin ajiye zantutukan ka/ki kafin wayar ka/ki ta bace, kana/kina iya samun damar dawo da zantuttukan ka/ki a baya.

 • Ajiyar zantuka na faruwa duk awa ashirin da hudu 24, tare da amfani da yanzar gizo.
 • Masu amfani da manhajar, baza su iya sakawa ko hana wannan tsarin ajiyar ba.
 • Masu amfani da manhajar, na iya hada sabon sashen ajiya ne kadai ta hanyar danna: “Jeri ” > Saiti > “Gyare-gyare” > “Ajiyar Zantuka”.
 • Kowanne sashe na da ma’ajiya daya, yayin da ka/kika kirkiri sabon ma’ajiyar zantuka, zata maye gurbin ma’ajiyar ka/ki ta da.
 • Ana iya dawo da ajiyayyun zantuka ne bayan an shiga/bude sashe! Da zarar an gama tantancewar lambobin na OTP.

Kwanciyar hankalin ka/ki

Zan iya karar abinda naga bai dace ba?

 

Burinmu kullum mu tabbatar da kwanciyar hankalin ka/ki, taimaka ka/ki kawo rahoton duk wani abu ko dabi’a da kake/kike ganin bai dace ba zuwa ga Ayoba.me/contact, sai ka/ki zabi “Kai karar wani mai amfani da manhajar”. Zamuyi bincike sannan mu zartar da hukunci idan da bukatar hakan.

Ka/ki sani cewa ba lallai mu iya sanar da kai/ke sakamakon binciken mu ba, amma na tabbatar maka/miki cewa muna daukan irin wadannan rahotannin da matukar muhimmanci.

Zan iya kawo karar wani ko wata da shima/itama ke amfani da manhajar?

Muna fifita kwanciyar hankalin masu amfani da manhajar mu sannan kuma bama yarda da al’adar batanci daga masu amfani da manhajar mu. Taimaka kaje/kije Ayoba.me/contact, sannan ka zabi “Kai karar wani mai amfani da manhajar”. Zamuyi bincike sannan mu zartar da hukunci idan da bukatar hakan.

Ka/ki sani cewa ba lallai mu iya sanar da kai/ke sakamakon binciken mu ba, amma na tabbatar maka/miki cewa muna daukan irin wadannan rahotannin da matukar muhimmanci.

TADI A AYOBA

Zan iya tura wa wasu bayanan sadarwar na lambobina ta yin amfani da Ayoba?

E zaka/zaki iya! Yi amfani da alamar + (alamar bude sabon shafin tadi) don fara sabon tadi, sannan ka/ki danna alamar jona abu, yanzu zaka/zaki iya zaɓan Lamba, sa’annan kawai ka/ki danna lambar sadarwar da kake/kike so ka/ki tura.

Zan iya tura sakon hotuna ta Ayoba?

Rarraba hotunan ka/ki da sauran hotuna da kafi kauna cikin sauki ta Ayoba. Yi amfani da alamar + (alamar bude sabon shafin tadi) don fara sabon tadi, Sannan ka/ki danna alamar jona abu (attachment), sanna ka/ki zabi sashen hotuna don zaban hotuna daga hotuna ka/ki. Za kuma ka/ki iya danna alamar kyamara dan daukar hoto da kuma tura shi nan take.

Zan iya tura inda nake ta Ayoba?

Tura inda kake/kike zuwa ga lambobin sadarwar ka/ki cikin sauki ta hanyar danna alamar + (alamar bude sabon shafin tadi) don fara sabon tadi, sa’annan ka/ki danna alamar jona abu (attachment), sannan ka/ki zabi ‘inda nake’.

Zan iya aika sakon murya ta cikin Ayoba?

Zaka iya aika saƙon murya gajere zuwa ga wani mai amfani na Ayoba cikin sauki ta hanyar danna alamar lasifika dake kusurwar dama daga kasan shafin tadi ka/ki. Za kuma ka/ki iya ƙirƙirar sabon tadi ta hanyar amfani da alamar + (alamar bude sabon shafin tadi) don fara sabon tadi, sa’annan ka/ki danna alamar jona abu, sannan ka/ki zabi Murya, sannan sai ka/ki danna alamar lasifika don daukar sakon ka/ki.

Ina bukatan aika fayil ko rubutacciyar takarda, zan iya amfani da Ayoba?

Aika sakon fayal-fayal ta hanyar danna alamar + (alamar bude sabon shafin tadi) don fara sabon tadi, sa’annan ka/ki danna alamar jona abu, sannan ka/ki zabi fayal. Yanzu duba cikin na’urar ka, zabo fayal din sannan ka turawa lambobin sadarwar ka/ki.

Yaya zan mai da martanin amsa na sakonni?

Danna sakon da kake/kike son gani. Idan zaka/zaki mai da martanin amsa, kawai danna sashen rubutu dake kasan fuskar na’urar ka/ki, sannan ka/ki rubuta martanin amsar ka/ki sannan ka/ki danna Tura. A saukake kamar haka.

Zan iya yada ko tura sakonnin da aka turo min zuwa ga lambobina na Ayoba?

Zaka/zaki iya tura rubutattun sakonni, fayal na murya, hotuna, da kuma lambobin sadarwa ta hanyar danne sakon da kake/kike son turawa, sannan sai ka/ki danna alamar kibiya ta turawa dake kusurwar dama da ke saman fuskar na’urar ka, sannan ka/ki zabi lambar da kake/kike son turawa sakon sannan ka/ki danna “tura”. Sakon zai je da alamar “Turowa akai”. Za kuma ka/ki samu sakon tunatarwa wanda ke nuna sakon ya turu.

Taya zan goge tsohon sako ko sakonnin da bana bukata?

Kawai ka/ki danne sakon dake kan shafin tadin, sannan ka/ki zabi alamar kwandon shara dake saman fuskar na’urar sannan daga karshe ka/ki tabbatar da zabin ka/ki.

Zan iya mayar da hirarraki na zuwa ga jerin ajiya?

A’a, Ayoba bashi da hanyar mayar da hirarraki zuwa ga jerin ajiya (a halin yanzu). Idan kana/kina son cire wata hira daga jerin hirarraki, zaka/zaki iya hakan ta hanyar goge ta, duk da cewa wannan gogewa ce ta dindindin kuma ba zaka/zaki iya dawo da ita daga baya ba.

Zan iya wawware hirarraki na ta hanyoyi daban daban?

Ana shirya maka/miki hirarrakin ka/ki bisa la’akari da wadda aka yi mafi kusa a koda yaushe, wadannan hirarrakin na bayyana ne daga saman jerin lis din. Ba zaka/zaki iya canja wannan tsarin jeren ba a Ayoba (a halin yanzu).

Ta yaya zan goge hirarraki?

Daga fuskar farko ta Ayoba, danne hirar da kake/kike son gogewa, sannan ka/ki zabi alamar kwandon shara dake saman fuskar, sannan ka tabbatar da zabin ka/ki.

Ta yaya zan kirkiri kungiyar tadi kuma na gayyaci lambobin sadarwa ta?

Danna alamar bude sabuwar hira + sanna ka/ki zabi “SABUWAR KUNGIYA”, sannan ka/ki debo lambobin da kake/kike son su kasance cikin kungiyar hirar ka/ki. Yanzu abinda kawai kake/kike bukata shine ka/ki fara tattaunawa.

Idan kuma ina son barin wata kungiyar hira fa?

Zaka iya ficewa daga kowacce kungiyar hira a kowane lokaci cikin sauki ta hanyar danna alamar kungiyar hira a saman shafin hirar ka/ki sa’annan ka zabi madannin “FITA DAGA KUNGIYA”, sannan sai ka/ki tabbatar da zabin ka/ki.

Idan kuma ina son goge wata hirar kungiya fa?

Don goge kungiyar hira, cikin sauki, danne kungiyar hirar akan ainahin fuskar manhajar, sannan sai ka/ki zabi alamar kwandon shara sanna ka/ki tabbatar da zabin ka/ki. Za kuma ka/ki iya zabar barin kungiyar a wannan lokacin.

Idan ka/kika goge wata kungiyar hira, zaka/zaki goge sakonnin kungiyar daga na’urar ka/ki ne kawai, amma bazai goge hirar ba a wayar sauran yan kungiyar.

Menene abubuwan da mai mallakar kungiya zai/zata iya yi?

Mai mallakar kungiya zai/zata iya kirkirar kungiya, ya/ta saka ko cire mutanen kungiyar.

Zan iya mai da wani/wata mai mallakar kungiyar?

Ikon Saffara kungiya bazai yuwu a mikashi ga wani ba

Za mu iya samun mai mallakar kungiya sama da mutum daya?

Baza ku iya samun mutane dayawa a matsayin masu mallakar kungiya ba.

An saka ni a wata kungiya, zan iya ganin tattaunar da akayi a baya?

Idan an saka ka/ki cikin wata kungiya, bazai yuwu kaga/kiga wata tattaunawa da aka yi a baya ba, sannan kuma da tattaunawar da aka yi kafin shigowar ka/ki kungiyar

To idan ina son dawo da hira ta data wuce fa?

An shirya ajiyar sakonnin ka/ki kai tsaye ya kasance a duk awanni 24, har idan kana/kina kan yanar gizo. Ba zaka/zaki iya hana wannan shirin ajiyar sakonnin na kai tsaye ba.

Zaka/zaki iya tilasta ƙirƙirar sabuwar ajiyar sakonnin ta hanyar danna karan Jeri (menu bar), zabi saiti, sannan gyare-gyare, sannan sai Ajiyar Hirarraki. Wannan zai ajiye maka/miki hirarrakin ka/ki cikin sirri a ma’ajiyar yanar gizo, sannan ya baka/baki damar sake dauko hirarrakin ka/ki idan bukatar hakan ta taso.

Don dawo da hirarrakin ka/ki ta hanyar danna madannin Jeri, sa’annan ka/ki zabi Saiti, sannan ka/ki danna Gyare-gyare ka/ki kuma zabi Ajiyar Hirarraki, sannan kuma Dawo.

Ka/Ki kula cewa ajiyar ka/ki ba a cikin na’urar ka/ki take ba, saboda haka zaka/zaki bukaci amfani da yanar gizo don yin ajiya.

 

Zan iya bada damar fayal-fayal su sauka da kansu idan an turo min?

Fasalin abubuwa su sauka da kansu a KASHE yake bisa yadda aka tsara manhajar. Idan kana/kina son hotuna da bidiyoyi da suka shigo maka/miki a manhajar su sauka da kansu, zaka/zaki iya kunna ‘Sauka da Kanka’. Za ka/ki iya kunna fasalin ‘sauka da kanka’ ta hanyar zaben ‘ainahin jeri’ (main menu), sannan sai ka/ki danna bangaren kayan kallo da sauraro, sannan sai ka/ki shirya ‘Sauka da Kanka’ ta yadda zai biya maka/miki bukata. Muna shawartar ka/ki kan cewa ka/ki bar wannan tsarin a kashe idan kana/kina amfani da data mai iyaka.

Hira da wadanda basa amfani da Ayoba

Zan iya yin hira da mutanen da basu da manhajar Ayoba?

Zaka iya aika saƙonni ta hanyar Ayoba ga kowa, koda kuwa basu da manhajar akan na’urar su. Saƙonni da aka aika wa mutanen da basu sauke manhajar Ayoba sunyi rijista ba, zai shiga ne ta fannin rubutaccen sako na SMS, kuma zai hada da wani adireshin yanar gizo don ganin sauran fayal-fayal din da kayan ciki idan akwai.

Munyi haɗin gwiwar da MTN, wanda yake nufin cewa masu amfani da MTN na iya mai da martanin amsa ga rubutattun sakonnin SMS na Ayoba, a kyauta, koda kuwa basu da manhajar Ayoba akan wayoyinsu. Wadanda basa amfani da MTN zasu samu sakonni daga Ayoba a matsayin rubutattun sakonni na SMS, amma ba zasu iya mai da martanin amsa ba. Muna kira ga wadanda ba sa amfani da MTN da su sauke manhajar Ayoba a kyauta daga Ayoba.me/download ko kuma a sashen manhajoji na Google.

Zan iya ƙara lambobin sadarwa, koda kuwa ba sa amfani da Ayoba?

Yayin kirkirar sabuwar hira, danna “Jeri” a kusurwar dama daga sama. Sannan ka/ki bada dama ga “Nuna lambobin sadarwa na SMS”. Yanzu zaka/zaki iya ganin dukkanin lambobin wayar ka/ki har wadanda basa amfani da manhajar Ayoba.

Idan wani daga cikin waɗannan lambobin ya sauke manhajar kuma ya yi rijista da lambar wayar da ke cikin lis din manhajar lambobin ka/ki, manhajar Ayoba din zai sabunta matsayin su kai tsaye ta yadda zai nuna cewa zasu iya mu’amalla a matsayin cikakkun masu amfani da Ayoba.

Zan iya tura hotuna ko fayal-fayal zuwa ga lambobin sadarwa wadanda basu sauke manhajar Ayoba ba?

Zaka/zaki iya aika hotuna, bidiyo da kuma adireshin yanar gizo zuwa ga lambobin da basu sauke manhajar Ayoba din ba. Wadannan lambobin sadarwa zasu karbi rubutaccen sakon tunatarwar na SMS wanda zai zo da adireshi don ganin abinda ke ciki. A kula cewa, kallo da/ko kuma sauke abin na iya janyo chajin data daga masu kamfanin sadarwa.

Na karbi sako da ga Ayoba, amma kuma ban da manhajar. Zan iya ganin sakon duk da haka?

Zaka/zaki iya ganin sakon rubutu da kuma fayal-fayal wanda wani mai amfani da Ayoba ya turo ta hanyar Ayoba, ko da kuwa baka/baki riga ka/kin sauke manhajar Ayoba ta kyauta din ba. Muna haɗin gwiwar da MTN, wanda yake nufin cewa masu amfani da MTN na iya mai da martanin amsa ga rubutattun sakonnin SMS na Ayoba ta yin amfani da sashen rubutu na SMS, a kyauta, koda kuwa basu da manhajar Ayoba akan wayarsu. Wadanda basa amfani da MTN, zasu samu sakonnin su daga Ayoba a matsayin rubutaccen sako na SMS, amma ba zasu samu damar mai da martanin amsa ba. Muna kira ga wadanda basa amfani da MTN dasu sauke manhajar Ayoba na kyauta daga Ayoba.me/download ko kuma Google Play Store.

SARRAFA LAMBOBIN KA/KI

Ta yaya zan iya ƙara lamba?

Kawai ƙara lambar zuwa lambobin sadarwa na wayar ka/ki. Da zarar ka/kin ƙirƙiri sabuwar lambar sadawarwa, zaka/zaki iya bude manhajar Ayoba din, danna alamar sabon saƙon + sannan ka/ki zaɓi lambar da kake/kike son yin tadi da ita.

Manhajar Ayoba din zai gano kai tsaye ko mai wannan lambar ya riga ya sauke manhajar kuma yayi rijistar lambar wayar sa tare da Ayoba. Idan ba haka ba, za su bayyana a matsayin lambobin sadarwa na Sako a cikin Ayoba.

Ta yaya zan goge lambobin sadarwa?

Zaka/zaki iya share lambobin sadarwa kamar yadda ka/kika saba, ta hanyar manhajar sadarwa ta wayar ka/ki. Buɗe jerin lambobin sadarwa na wayar ka/ki, danna sunan mai lambar sannan kuma sai ka/ki danna jeri a kusurwar hannun dama daga sama. Zaɓi ‘goge’, sannan ka/ki tabbatar da zaɓin ka/ki.

Ta yaya zan iya toshe lamba?

Zaka/zaki iya toshe lamba a Ayoba cikin sauki ta hanyar tadi sannan sai ka/ki danna alamar Jeri a kusurwar hannun dama daga sama. Zaɓi Toshewa, sannan ka/ki tabbatar da aikinka. Da zarar ka/kin toshe wata lambar sadarwa ba zaka/zaki cigaba da samun saƙonni ko abubuwa daga wannan lambar ba, sannan shi/ita ma ba zai/zata iya ganin matsayin ka/ki ba. Zaka/zaki iya cigaba da ganin lambar a cikin jerin lambobin sadarwar ka/ki, amma tare da alamar “An toshe”. Idan kana/kina son aikawa da karɓar saƙonni daga lambar da aka toshe, dole ne ka/ki bude lambar.

Muna so mu tabbatar da zaman lafiyar ka/ki a kowanne lokaci, don haka a taimaka a bayar da rahoton duk wani abun da bai daceba ko dabi’ar da bata dace ba a Ayoba.me/contact, ko kuma a tuntubi <FAQ Security Section> a nan

Ta yaya zan bude lambar sadarwar da aka toshe?

Zaka/zaki iya bude lambar da aka toshe a baya ta hanyar ƙirƙirar sabon taɗi ta hanyar amfani da alamar + , zaɓi lambar sadarwar, yi amfani da jerin da ke kusurwar dama daga sama sannan ka/ki danna ‘bude’, sannan ka/ki tabbatar da aikin ka/ki. Yanzu za ka sake iya yin tadi da wannan lambar sadarwa, wannan lambar sadarwa itama za ta iya aiko da sababbin saƙonnin kuma ta amsa maka/miki saƙonnin ka/ki, sannan kuma ta ga matsayin ka/ki.

Ta yaya zan iya yin kira na murya akan Ayoba?

Zaka/zaki iya yin kira na murya daga manhajar ta Ayoba zuwa ga duk wata lambar sadarwarka ta Ayoba. Za’ayi cajin kiran a matsayin ainahin kira na murya kuma yana amfani da kudin wayar ka/ki ko mintunan da ke da akwai. Abu mafi mahimmanci, yin kira a cikin manhajar ba ya amfani da data kuma ba kyauta bane. Don yin kiran murya ta amfani da Ayoba, danna + (alamar sabon taɗi) sannan sai ka/ki danna alamar waya don yin kiran murya.